Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamomin Cutar Zazzabin Lassa Da Matakan Da Ya Kamata a Dauka


Wasu jami'an kiuwon lafiya da ke kula da wani da ya kamu da cutar zazzabin Lassa
Wasu jami'an kiuwon lafiya da ke kula da wani da ya kamu da cutar zazzabin Lassa

Cutar zazzabin Lassa, cuta ce da aka fi danganta wa da beraye ko kuma gafiyoyi, wacce ke saurin daukan rai idan ba a dauki matakan gaggawa ba, lamarin da ya sa jami'an kiwon lafiya da hukumomi ke wayar da kan jama'a kan yadda za a guje wa wannan cuta.

Cutar zazzabin Lassa wata cuta ce da ta samo asali daga wani gari da ake kira Lassa a jihar Borno, cutar na yaduwa ne a duk wani abu da bera ya samu kusantar shi, musamman abinci.

Alamomin cutar sun hada da yadda mutane za su dinga jin zazzabi, ciwon kai, da kuma amai daga lokaci zuwa lokaci inji Dr. Mustapha Mannir, na jami’ar Pittsburgh da ke nan Amurka.

Dr. Mustapha, ya kara da cewa hanyoyi da akan iya kamuwa da cutar da sun hada da yadda mutane ke ajiyar kayan abinci ba tare da kulawa da su ba wanda hakan kan iya bai wa beraye damar lalata abinci.

Masana na ganin cewar a duk lokacin da mutane suka ajiye abubuwan amfaninsu, da akwai bukatar sake tsaftace su kafin amfani da su don guje wa kamuwa da cutar.

Dr. Mustapha ya kara da cewar a duk lokacin da bera ko gafiya da duk sauran namun daji suka yi fitsari ko kuma kusanci abincin da mutane kan ci, akwai tabbacin za’a iya kamuwa da cutar ba tare da bata lokaci ba.

A karshe ya ce akwai bukatar mutane su dauki matakin garzayawa zuwa asibiti da zaran sun fara jin wani canji a jikinsu ko dai na ciwon kai da zazzabi ko wasu kuraje.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG