Boko Harama ta Kai Hari Kan Coci a Jahar Barno ta Kashe Akalla Mutane 24

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da suka tsere daga hanun 'yan boko haram da suka yi garkuwa da su

An kai harin ne kusa da Chibok garin da 'yan bindiga suka kama 'yan mata su fiye da 200 cikin watan Afrilu.

Mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga daga kungiyar masu tsatsaurar ra’ayin addinin Islama da ka fi sani da Boko Haram, sun kai hari kan wasu majami’u masu yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya jiya lahadi, suka kashe akalla mutane 24.

Jami’ai a yankin da kuma shaidun gani da ido, sun ce ‘yan bindiga kan babura sun kai hari kan kauyukan da suke kusa da garin Chibok a jahar Barno. Shaidun gani da idon suna zargin sojojin Najeriya da sanyin jiki wajen daukan matakai nan da nan kan irin wadannan hare hare.

Babu dai wata kungiya ko mutum d a ya fito nan da nan ya dauki alhaki kai wadannan hare hare.

A cikin watan Afrilu kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan mata su fiye da metan a wata makaranta dake garin Chibok. Jami’an gwamnati suka ce har yanzu ba a san inda fiyeda 219 na ‘yan matan suke ba.