Dama dai tun a baya ne aka yi ta yayata jita-jitar cewa mayakan kungiyar ta Boko haram sun kafa sansani a jihar Nejan mai iyaka da Abuja fadar gwamnatin Najeriya.
A yanzu dai gwamnan jihar Nejan Alh. Abubakar Sani Bello ne da kansa ya tabbatar da cewa, mayakan kungiyar ta Boko haram sun kafa tutocinsu a wasu garuruwa na yankin karamar Hukumar Shiroro da Muya.
Sh ma shugaban wata kungiyar matasa a yankin na shiroro, Jibrin Abdullahi Tafidan Alawa, yace a yanzu haka yan kungiyar ta Boko haram sun kame mazabu guda 7 daga cikin 8 dake cikin karamar Hukumar Shiroron..
Jihar Nejan dai ta zama wani sansani na 'yan ina da kisa inji wani mazaunin garin Gulbin Boka a yankin karamar hukumar Mariga da ya nemi a sakaya sunansa yace ko a daren ranar lahadin nan maharan sun kashe masu mutane 11 tare da kore masu shanu masu tarin yawa.
A yanzu dai da dama daga cikin manyan garuruwa a jihar Nejan makare suke da 'yan gudun hijira da suka tsere daga kauyukkansu saboda hare haren yan bindigar.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5