BOKO HARAM: Marayu da Mata da Suka Rasa Mazajensu Suka Dawo daga Kmaru

Wasu cikin yaran da Boko Haram ta kashe iyayensu

Wasu cikin wadanda Boko Haran ta daidaita da kashe iyayensu da mazajensu da kuma kone muhallansu sun dawo daga Kamaru suna Adamawa.

Yaran marayu da suka dawo daga garuruwa daban daban suka fito. Yayin da wasu suna da dan wayon sanin sunan garinsu wasunsu kuma basu san koina ba.

Wani yaro Zubeiru yace garinsu Madagali ne cikin jihar Adamawa. Lokacin da yake gudun hijira a bakin kasuwa yake. Da yayi rashin lafiya wani ya kaishi asibiti. A cikin wani masallaci dake kusa da kasuwar yake kwana.

Wani Dahiru Muhammad dan shekara goma yana cikin yaran da Boko Haram ta rabasu da iyayensu yana kuma cikin yara talatin da takwas da suka dawo Najeriya daga Kamaru bayan sun kwashe watanni tara..

A sansanin 'yan gudun hijira dake mijami'ar Katolika ta St. Theresa dake Yola mafi yawan wadanda ke zaune a wurin yara ne da basu da iyaye. Akwai kuma mata da aka kashe mazajensu aka barsu da yara.

Talatu da Ladi Joseph 'yan shekaru goma sha biyar da sha uku da suka rasa iyayensu da kannensu cikin hare-haren Boko Haram sun shaida cewa bayan ci da sha da mijami'ar Katolika ke basu ta tsara masu darusa da basu shawarwari akan yadda zasu tafi da rayuwarsu.

Wasu cikin yaran an sa sun cigaba da karatunsu a makarantun firamare tare da shirya masu abun yi domin rage masu kewar iyayensu.

Ita mijami'ar Katolika tace ta rungumi shirin taimakawa marayun da gwaurayen wajen shata masu ingartacciyar shimfida saboda rayuwarsu nan gaba.

Kawo yanzu hukumar bada taimakon gaggawa bata kammala tantance adadin marayu ba.

Ga karin bayani daga Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

BOKO HARAM: 'Yan Gudun Hijira Marayu da Mata da Suka Rasa Mazajensu Suka Dawo daga Kamaru