Kasar Kamaru ta fara maido yan Nigeria wadanda suke gudun hijira a kasar. Wadanda suka fara isowa ta garin Sahuda dake kan iyakar Nigeria da Kamaru a jihar Adamawa arewa maso gabashin Nigeria, jami'an tsaro sun tantance su kafin hukumomin agaji suka karbe su.
Shugaban hukumar bada tallafi ta jihar Adamawa, Alhaji Haruna ya shedawa sashen Hausa cewa sun samu takarda daga hukumomin kasar Kamaru cewa zasu maido da 'yan Nigeria, wadanda suke gudun hijira a kasar su.
Yace a takaice dai bayanan takardun da suka samu daga hukumomin Kamaru suna nuni da cewa kimamin yan gudun hijira dubu 12 za'a maido.
Amma yace ba lokaci daya bane za'a dawo dasu. To amma yace a yanzu an fara kawo 'yan gudun hijira sahu biyu zuwa Sahuda dake kan iyakar Nigeria da Kamaru.
Alhaji Haruna yace da farko sun dauko mutane 516, kuma abinda aka sabawa yiwa 'yan gudun hijira, shi aka yi musu ta wajen kula da lafiyar su da sauran hidimomi.