Shugaban wanda yake magana a babban taron Ahlus Sunnah karkashin Izala da majalisar musulunci ta duniya Rabi'atul Alami Islami a Abuja, yace tun taron rantsar da shi ya kore ‘yan Boko Haram daga wata alaka da Musulunci. Yana mai cewa yawancin kungiyoyin ta’addancin duniya na fakewa da sunan Musulunci ne, inda kuma mafi yawan wanda suke kashewa Musulmi ne.
Shugaba Buhari ya nanata kudirin gwamnatinsa na gamawa da Boko Haram, yana mai kira ga malamai su kara dagewa wajen fadakar da mabiya illar miyagun akidu. Shima shugaban majisar Musulmi ta Duniya Rabi'atul Alami Islami, Sheik Abdallah Mohsen Al-Turki, ya nesanta da alaka da ayyukan ta’addanci, yana mai cewa sakon musulunci shine tabbatar da adalci a doron kasa.
Al-Turki ya yabawa shugaba Buhari saboda bunkasa kyakykyawar alaka Tsakaninsa da sarki Salman na Saudiyya, shugaban Izala Shiek Abdullahi Bala Lau a gurin taron ya nanata kudirin malamai na ci gaba da wa’azi wajen wayar da kan al’umma sahihiyar akidar Islama, inda take ya yabawa yunkurin shugaba Buhari na yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawar da yan ta’adda.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5