Biyo bayan kisar gilla na gomman manoman shinkafa a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya da mayakan Boko Haram su ka yi, Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wani zama na musamman dangane da kalubalen tsaro dake ci gaba da dabaibaye Najeriya.
Majalisar ta nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami manyan
Hafsoshin sojojin kasar tare da aiwatar da dukkannin bukatun da
Gwamnan jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ya gabatar.
Cikin bukatun da gwamnan ya mika akwai neman Najeriya ta nemo sojojin
haya don su yi mata yaki da Boko Haram, kuma a cewar Sanata Kaita ai a
baya an yi hakan kuma an sami nasara; don haka, shi ba abin da ba zai
goyi baya ba muddin za a sami sauki daga wannan kashe kashen talakawa
da ake yi a kasarnan.
Amma a cewar wani masanin tsaro farfesa Mohammed Tukur Baba, ba fa za a
ce sojojin Najeriya sun gaza ba, ko ba za su iya wannan yaki ba, akwai
dai wani abin da ke kawo masu cikas da ya kamata a bincika.
Yana mai cewa sojojin gwamnati na da duk kwarewar da za su tunkari
wannan masifar kuma su yi nasara. Farfesan ya ce akwai hatsari mai yawa
a shigowa da sojojin haya.
Cikin sakon da ya wallafa, Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin NajeriyaJanar Tukur Buratai ya ce ba a fahimci yadda ainihin matsalar
ta'addanci ta ke bane. Ya na mai bayanin cewa akwai yiwuwar ta'addanci a
Najeriya ya kai karin shekaru ashirin nan gaba idan ba a dau matakin da ya dace ba.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5