Boko Haram: An Cewa Mazauna Legas Su Sa Ido

Fasinjoji na shiga motar haya ta bas a jahar Legas

Jami’an tsaro da shugabannin al’uma a jahar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, sun yi kira ga mazauna garin da su sa ido domin gano ‘yan Boko Haram da ake zargi suna kwararara zuwa kudancin kasar.

Bayan wani taro da aka gudanar tsakanin shugabannin al’umomin jahar da rundunar ‘yan sanda, daya daga cikin shugabannin al’umar arewacin kasar mazauna Legas da ya halarci taron, Alhaji Mustafa Mai Kanuri Bei, ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sanda Jahar, Mr. Fatai Oyeseyi, ya ce lallai akwai ‘yan kungiyar Boko Haram da ke shiga garin.

“Mun tabbatar Boko Haram na zuwa garin nan wadansu suna boye su, mun tabbatar akwai Boko Haram garin nan.” In ji Alhaji Mustafa.

Yanzu haka dai shugabanin al’umar sun yi ikrarin cewa suna daukan matakan kariya domi dakile duk wani yunkuri da zai kawo barazana ga jahar.

“Muna da jami’an tsaro kusan guda tamanin, wadanda suke a cikin kasuwar mu, sannan kuma mun saya musu wannan abun da ake duba mutane." A cewar Alhaji Sarki Ummaru Na Gwaggo, wanda shima ya halarci taron.

Sai dai wasu daga cikin shugabannin al’umar mazauna arewacin kasar a garin na Legas, kamar irinsu Alhaji Ado Dan Sudu, cewa su ka yi “idan har za su (jami'an tsaro) kira taro domin tabbatar da tsaro a kasa to a kira kabilan nan uku, kada a ware wata kabila ita kadai, domin hakan na nufin ana zargin ita wannan kabila ke nan.”

Jahar Legas ta kasance jaha mafi hadahadar kasuwanci a Najeriya, tare da hada kabilu daban daban daga sassan kasar da ma wasu kasashen nahiyar Afrika kasancewar ta na bakin teku.

Ga karin bayani a wannan rahoto na wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril:

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram: An Cewa Mazauna Legas Su Sa Ido 2’14”