Biyu Sun Mutu An Ceto 38 Daga Wani Jirgin Ruwa Na Bakin Haure Kusa Da Tsibirin Canary A Spain

Bakin Haure - TsibirinCanary, Spain

Masu aikin ceto a tekun kasar Spaniya sun ce sun ceto mutane 38 da ransu tare da samun gawarwakin wasu biyu daga cikin wani kwale-kwalen bakin haure da ya taso daga yammacin Afirka ya ke kokarin isa tsibirin Canary.

WASHINGRTON, D. C. - Wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa ne ya hango jirgin mai nisan mil 76 (kilomita 140 ko 87) da kudancin Gran Canaria da yammacin jiya Litinin.

Bakin Haure da suka kai Spain

An kwashe mutane hudu da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibiti a cikin jirage guda biyu masu saukar ungulu, yayin da aka kai wasu 34 zuwa tashar jiragen ruwa na Arguineguín, in ji ma'aikatar ceto ta tekun Spaniya. Daga cikin wadanda suka tsira har da mata bakwai.

Hukumomin kasar dai na kokawa kan karuwar bakin haure da ‘yan gudun hijira masu tasowa daga yammacin Afirka da ke isa tsibirin wanda ya zamana wata hanya ce musu ta shiga nahiyar Turai.

Bakin Haure - Spain Canary Islands

Kusan mutane 12,000 ne suka tsere daga talauci, rikice-rikice da rashin zaman lafiya a yammacin Afirka suka isa Canaries a cikin watanni biyu na farkon shekarar nan, a cewar ma'aikatar cikin gida ta Spain, hakan ya ninka adadin wadanda suka biyo wannan hanya sau shida idan aka kwatanta da wannan lokaci a bara.

Galibin bakin hauren dai sun taso ne daga gabar tekun kasar Mauritania a kan kwale-kwalen kamun kifi na fasaha da aka fi sani da Pirogues kuma suna tafiya na kwanaki da dama a kan ruwa da iska mai karfi ga kuma igiyar ruwa ta Atlantic. Yayin da dubbai sukan tsira daga balaguron haɗari, da yawa suna mutuwa ko ɓacewa inda daga baya ragowar gawarwakin wasu ke gangarawa zuwa gefen Tekun Atlantic.

Spain ta ceto wasu bakin haure a Canary Islands

A makon da ya gabata, an gano wasu jiragen biyu kan Teku da suka taso daga Mauritania zuwa kasar ta Spain inda jirgin na su ke yawo ya nisanta da daruruwan mil (kilomita) daga kusa da tsibirin Cape Verde, bayan da suka kasa isa inda suka nufa, in ji ‘yan sanda.

An ceto mutane 11 daga cikin kwale-kwale guda da kuma wasu biyar daga cikin na biyun duk da cewa mutum daya ya mutu daga baya. An kuma gano gawarwakin mutane biyar sannan wasu da dama kuma ana kyautata zaton sun bata a teku.

-AP