A cikin hirarsu da Jummai Ali. Profesa Boube Na Maiwa na jami’ar Diop, Dakar, kasar Senegal ya bayyana cewa, ganin yadda wadansu suka rika yin haka a lokuta bayan ana bayansu kudin fansa, yana daya daga cikin dalilan da ake yawan garkuwa da jama’a. Yace neman kudin banza da arzikin daren daya na iya sa zauna gari banza shiga irin wadannan ayyukan.
Yace na biyu kuma, idan aka sami yanayi na tashe tashen hankali da ayyukan ta’addanci kamar yadda Najeriya ke fuskanta, to yana yiwuwa masu irin wadannan aika aikan su shiga sace wadanda suke gani suna iya hana ruwa gudu a al’amuran nasu. Yace irin wadannan mutanen suna kuma iya sace wadanda suke gani zasu iya samun kudi daga garesu domin sayen makaman da suke amfani da su ko kuma domin su yi garkuwa da su.
Rundunar sojin Najeriya ta sanar jiya Lahadi cewa, an sace Kanal Sama’ila Musa daya daga cikin manyan jami’an makarantar horas da sojojinta dake Jaji garin Kaduna, bayanda wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba suka tare motar da yake ciki da iyalinsa, suka fitar da ita daga motar kafin suka shiga suka arce da shi.
Lamarin ya faru ne ranar asabar da misalin karfe bakwai da rabi na yamma. Hukumomi suna kira ga al’umma su sanar da ofishin jami’an tsaro mafi kusa idan suna da wani bayani dangane da lamarin.
Yan fashin dai sun arce ne a bakar mota kirar marsandi mai lamba. KUJ 154 TZ.
Ga cikakken bayanin Prof Boube Namaiwa
Your browser doesn’t support HTML5