Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya wani faifan bidiyo ya bayyana da "Abubakar Shekau" yana jawabin yin murabus


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau,

Jiya Alhamis wani faifan bidiyo ya fito a kafar You Tube inda aka nuna wani wai shi Abubakar Shekau shugaban Boko Haram yana jawabin da ya yi kama da yin murabus

A jiya Alhamis, wani sabon faifan bidiyo ta shafin YouTube a internet ya bayyana dauke da wanda ake cewa shine shugaban Boko Haram wato Abubakar Shekau, inda ya ke jawabin da ke alamta yin murabus dinsa.

Bidiyon na mintuna 8 ya nuna Shekau a zaune a cikin natsuwa yana jawabin yabo ga mayakan sa kan kungiyar, wanda a karshe yayi jawabin da ke nuna mika wuyansa da cewa, “Ni kam a wajena karshen abin kenan”.

Sai dai bai yi wani karin bayanin abinda yake nufi ba. A fayafayen bidiyon Shekau da suka gabata, an saba ganinsa yana hargowa da harba bindiga sama tare da yin barazana ga makiyan ‘yan Boko Haram.

Wani shugaban kamfanin tsaro a Jamus ‘Yan St. Pierre yayi tsokacin cewa, wata kila Shekau na nuni ne ga shirin sauya shugabancin kungiyar ta Boko Haram. Mista Yan yace, kila yana kokarin nuna musu wata sahihiyar mafita ne da zasu sami sabon jagora bisa irin nasu tsarin na shugabanci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG