Matakin da birnin kudancin jihar California ya dauka, birni na biyu mafi yawan jama'a a Amurka bayan birnin New York, ya biyo bayan alkawarin da shugaba Donald Trump ya yi na aiwatar da korar bakin haure.
Dokar ta tanadi kariya ga bakin haure a cikin dokokin birnin. Dan majalisar Paul Krekorian, ya ce matakin ya magance “bukatar tabbatar da cewa al'ummar mu baki a nan Los Angeles sun fahimci cewa mun fahimci damuwarsu.”
Masu zanga-zangar da ke goyon bayan bakin haure sun yi magana a kan matakan majalisar birnin Los Angeles kafin kada kuri'a, suna rike da alluna da ke cewa, “Los Angeles Ta Zama Wurin Kariyar Bakin Haure Yanzu!” Suna ta fadi a cikin yaren Spanish cewa “Me muke so? Wuri Mai Kariya. Yaushe muke so? Yanzu.”
Mambobin majalisar sun ce birnin na da bakin haure miliyan 1.3, ba tare da bayyana adadin mutanen da suka shiga kasar ba bisa ka'ida.
Jihohi 11, sun dauki matakai daban-daban, don rage hadin gwiwa da hukumar kula da shige da fice ta gwamnatin tarayya, a cewar Cibiyar lauyoyi mai zaman kanta. Trump, wanda ya lashe zaben ranar 5 ga watan Nuwamba, zai fara aiki ranar 20 ga watan Janairu.
Tawagar mika mulki ta Trump ba ta amsa bukatar yin sharhi ba.