Birnin Damagaram Zai Karbi Bakuncin Bikin Samun ‘Yancin Kai

Farai Ministan Nijar Brigi Rafini Na Jawabi A Gasar Kokawar Takobin Nijar

An zabi birnin Damagaram a matsayin birnin da zai karbi bakuncin bikin zama Nijar jamhuriyya na wannan shekara.

Firai Ministan Jamhuriyar Nijar, Birji Rafini, ya kaddamar da fara aikin sallar Damagaram sabuwa da za a yi ranar 18 ga watan Disamba,

Wannan rana ita ce ranar da Nijar ta zama Jamhuriya, inda ake sa ran a wannan shekaran birnin Damagaram ne zai karbi bakuncin bikin.

“Dole a kama aiki fiye da yadda aka yi a Maradi da Doso da Tahou, ya zamanto Damagaram, ya zama babban birni.”

Firai minitsan ya kara da cewa “kowa ya san cewa, Zinder, garin tarihi ne.”

Mansour Haji Dodo, minista mai ba da shawara a fadar shugaban kasa, wanda shi ne shugaban kwamitin gina birnin ya ce za a bai wa ‘yan kasuwa dama su kawo gudunmawarsu wajen gina birnin na Damagaram.

“Za a ba su dama su shigo da kayayyakin gini, ba tare da sun biya kudin haraji ba, wannan shi ne gudunmuwar gwamnati.” Inji Ministan.

A duk shekara, akan zabi birni guda a matsayin wanda zai karbi bakuncin bikin zama kasar ta Nijar Jamhuriyya.

Saurari rahoton Tamar Abari domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Birnin Damagaram Zai Karbi Bakuncin Bikin Samun ‘Yan cin Kai - 2'34"