Kamar yadda wakilin Sashen Hausa a Niamey, Sule Mummuni Barma ya fada; karo na hudu a kasa da watannin biyu, kungiyoyin fafitika a jamhuriyar Nijer sun gudanar da zanga zanga a ranar lahdi 25 ga watan fabreru, da nufin tilastawa ma’ikantar kasar su canza ra’ayi akan dokar harajin 2018, wace tuni talakawa suka fara korafi akan yadda ta haddasa tsadar rayuwa.
A gangamin shugabanni suna ci gaba da bayyana damuwa kan irin wahalhalu da wannan kasafin kudi, wadda a ciki hukumomi suka tsawwala haraji kan al'umar da tuni take fama da mawuyacin hali.
Wani mai magana da yawun gamayyar jam'iyun da suke cikin gwamnati, yace idan aka lura, babu inda ake zanga-zanga a duk fadin Nijar, sai a Niamey, inda kamar yadda yake cewa, nan ne cibiyar 'yan adawar kasar.
Ya kara da cewa ai da zanga zangar da farar hula ce da tuntuni gwamnati ta saurare su.
Ga karin bayani daga rahoton Sule Barma.
Facebook Forum