Binciken Rasha: Trump Ya Nuna Fushinsa Kan Janyewar Sessions

Shugaban Amurka, Donald Trump

Ga dukkan alamu janyewar da babban Atoni Janar din Amurka Jeff Sessions ya yi, daga binciken zargin katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka a bara, bai yi wa shugaba Donald Trump dadi ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada wa jaridar New Yorks Times cewa muddin sabon mai binciken rawar da ake zargin Rasha ta taka a zaben shugaban kasa ko kuma ta hada kai da tawagar kamfe din sa a bara, mai wannan binciken "ya wuci makadi da rawa."

Trump ya kara da cewa idan aka fadada binciken har ya hada da harkokin kasuwancin iyalinsa da ba su shafin batun Rashan ba, ba zai yarda da wannan ba, saboda haka a cewar Trump ya nuna an wuce ka’ida.

Shugaba Trump yana wannan maganar ne a cikin wata doguwar hira da ya yi, inda ya bayyana mamakinsa kan matakin da Atoni Janar na Amurkan Session ya dauka na ganin ya nesanta kansa daga wannan bincike da ake yi game da kasar Rasha.

"Sam bai kamata a ce Sessions ya janye jikinsa daga wannan batu ba, da ya san zai yi haka da ya fada min kafin ya karbi aikin." In ji shugaba Trump.