Binciken Kotun Duniya Zai Shafi Wasu Mutane Har 6 A Ivory Coast

Babban lauyan shigar da kara a kotun duniya, Luis Moreno-Ocampo ya na gaisawa da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara a birnin Abdidjan.

Za a binciki wadanda su ka fi kowa laifi a rikicin kasar Ivory Coast inji babban lauyan kotun duniya Luis Moreno-Ocampo.

Babban lauyan shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ya ce za a gudanar da bincike game da wasu mutane shidda bisa zargin da ake yi mu su da taka rawa a cikin mummunan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da aka yi kasar Cote d’Ivoire.

Luis Moreno-Ocampo ya fada da yammacin jiya Asabar cewa binciken da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya za ta yi zai maida hankali ne a kan wadanda aka yi amanna cewa sun fi kowa laifi a cikin rikicin. Kuma ya ce masu binciken ba su san ko su waye wadannan mutanen ba.

Kwanan nan kotun ta bada izini a gudanar da bincike akan yiwuwar aikata manyan laifuffukan yaki a kasar Cote d’Ivoire, inda aka ce an kashe mutum kusan dubu 3 lokacin da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ya ki mika mulki ga Alassane Ouattara wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi.

Mazauna unguwar Yopougon a birnin Abidjan su na tsaye a wani wurin da ake zargin cewa an binne dimbin gawarwaki a ciki.