Binciken Da Fifa Ke Ma Sepp Blatter Na Iya Daukar Lokaci Mai Tsawo

Akwai yiwuwar daukar akalla shekaru biyar kafin a iya gabatar da wata kara a kotu daga binciken da ake gudanarwa akan shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya da aka dakatar wato Sepp Blatter.

Ana tuhumar tsohon shugaban mai shekaru 79 da haiyuwa ne da zargin karbar cin hanci da rashawa a shirye shiryen wasannin cin kofin duniya na shekarar 2018 da 2022 daga kasar Rasha da kuma Qatar.

A cikin watan maris da ya gabata ne , jamian tsaro suka mamaye shelkwatar hukumar dake Zurich inda suka damke wasu manyan nma’aikatan hukumar su bakwai.

A yanzu haka dai ofishin babban lauyan hukumar na ci gaba da bincike kan lamarin sai dai kuma binciken na iya daukar wani lokaci mai tsawo.

A cewar mai Magana da yawun ofishin babban lauyan hukumar Andre Marty “wannan babbar matsala ce mai sarkakiyar gaske , kuma binciken zai iya daukar shekaru a kalla biyar kafin a gabatar da su gaban kuliya, har ma idan hakan ta iya faruwa Kenan”

Ya kara da cewa “har yanzu bamu kaiga cimma wata matsaya ba da zamu iya gurfanar da kowa gaban kuliya, kuma bamu iya bada takamaima lokacin da hakan zai faru. Matakin da muke a yanzu shine, kokkarin harhada bayanai da kuma bin diddigin lamarin musamman a game da wasanin cin kofin duniya na shekarar 2018 da 2022.