Wani bincike da aka wallafa sakamakon sa jiya Laraba wanda yake bayyana cewar kimanin kaso biyu cikin uku na iyaye sun nuna damuwar su akan yadda ‘ya’yan su matasa ke kashe lokaci akan wayoyin hannu.
Binciken da cibiyar Pew Research Center ta gudanar ya bayyana cewar, kashi ukku na iyayeyn sun bayyana tasu damuwar ne akan yadda iyaye ke daukar lokuta masu tsawo akan wayoyin hannu.
A bangaren matasan kuwa sun ayyana cewar sau dayawa iyayen su kandauki wayoyin su da har basu duba ko maida hankalin su a dai-dai lokacin da suke da bukatar tattauna wasu matsalolin da suka shafesu. Binciken ya kira danganta tsakanin matasa da wayoyinsu da sabon suna ‘mutu ka raba’ a turance kuwa ‘hyperconnected.’
Kashi uku cikin hudu kuwa na matasa kan duba wayoyin su cikin kankanin lokaci a koda yaushe, kodai domin duba sako ko kuma aikawa da sako a kafofin yanar gizo. Haka suma iyaye sukan yi wannan dabi’ar cikin kowane irin yanayi suke.
Manyan kamfanoni fasaha na cigaba da fuskantar matsin lamba, dangane da yadda duniya ke cigaba da daukar sabon salo, inda mutane basu iya rayuwa saida na’urorin zamani.
Matasa kuwa sun dau alwashin kawo canji, kashi 52% sun bayyana cewar sun rage mu’amalar su da wayoyin zamani, su kuwa wasu kaso 57 sun bayyana cewar sun rage amfani da shafukan yanar gizo.