Kasashen duniya na samun gagarumar nasara ta bangarorin mace-macen yara, da cutar HIV da kuma matsanancin talauci, amma idan Amurka da wasu kasashen suka janye taimakon agajin da suke badawa, wannan ci gaban zai rage, a cewar Bill Gates, mai kamfanin Microsoft.
A yau Laraba ne gidauniyar Gates ta fidda rahoton sakamakon abubuwan data ke yi na shekara-shekara karon farko, wanda kuma yi hasashen abubuwan da zasu faru na da shekarar 2030 bisa wadannan ma’aunan, tare da yin la’akari kuma da wasu muhimman abubuwa kamar samar da kudade.
An yiwa rahoton taken “Goalkeepers”. Bayannan da gidauniyar ta Gates ta samo tare da taimakon cibiyar alkaluman kiwon lafiya ta jami’ar Washington, sun nuna an sami gagarumin cigaba a muhimman bangarori.
An samu raguwar yawan yara dake mutuwa, da mace-macen da suka danganci Cutar dake karya garkuwar jiki, da suka ragu da kusan rabi tun bayan shekarar 2005.
Haka kuma an samu raguwar talauci daga kashi 35 zuwa kashi tara daga cikin dari.
A lokacin wani taro da aka yi ta wayar tarho, Gates ya danganta nasarorin da aka samu da kokarin da gwamnatocin duniya suka yi don tunkarar matsalolin, da kuma yin sabbin dabarun jinya.