Adadin mace-mace sanadiyyar babbar girgizar kasar nan da ta daidaita kudancin Mexico ya karu zuwa 90, kuma mace-macen ya fi aukuwa ne a jahar Oaxaca (pron.: Wahakaa)
Babbar girgizar kasar, mai karfin 8.2 a ma'auni, ta bararraka gabar kudu mai nisa na tekun Atlantica, daf da tsakar daren ranar Alhamis, mai tazarar kilomita wajen 100 daga garin Tonala.
Zuwa jiya Lahadi da yawa daga cikin mutanen wurin sun cigaba da kasancewa a waje saboda tsoron kar hucin girgizar kasar ya rutsa da su, ciki har da wanda ya auku da safiyar jiya Lahadi mai karfin 5.2 a ma'auni.
Jami'ai a jahohin Oaxca (Wahakaa)da Chiapas sun ce dubban gidaje da kuma daruruwan makarantu sun lalace au sun rushe. Rahotanni na nuna cewa dubban mutane ba su da ruwa.
Shugaban Mexico Enric Pena Nieto ya ce wannan girgizar kasar ta fi ta 1985 wadda ta hallaka dubban mutane. A wani jawabinsa da aka yada da yammacin ranar Jumma'a, ya ayyana ranaku uku na makoki a kasar baki daya sannan ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta taimaka a farfado.
Facebook Forum