Bikin Kirsimeti: ‘Yan Kasuwa Da Dillalan Dabbobi Sun Koka Da Rashin Ciniki A Accra

Kasuwan dabbobi

A cewar 'yan kasuwar, ko da yake sun sami ƙarancin ciniki a bara, amma wannan shekarar ta fi muni.

'Yan kwanaki kadan kafin gudanar da bukkukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, ‘yan kasuwa da dillalan awaki da tumaki sun koka da rashin ciniki a Accra, babban birnin Ghana.

A cewar 'yan kasuwar, ko da yake sun sami ƙarancin ciniki a bara, amma wannan shekarar ta fi muni.

A yayin da wasu ‘yan kasuwan suke danganta karancin cinikin da tsadar kaya da rashin kudi a hannun jama’a, wasu kuma sun nuna damuwa kan tasirin da kalandar ilimi na bana ya yi a kasuwancin su a wannan lokacin bukukuwan.

Kasuwan Makola

Hasiya tana sayar da kananan tufafin sawa na zamani ne a kasuwar Makola dake Accra. Ta ce: Muna zaune, ba a sayan komai. A da warhaka mutane suna rike yara uku zuwa hudu ne su zo su siya musu kaya, amma yanzu dai babu ciniki.

Haniyatu tace: "Shekarar da ta wuce, ciniki ya yi dadi, amma wannan shekarar dai to … muna jira dai."

Adama AbdulKareem, tana sayar da kayan abinci ne a kasuwar Makola da ke cikin kwaryar birnin Accra, ita ma ta jaddada tasirin bude makarantu a wannan watan da rashin cinikinsu.

"Muna ganin shekarar da ta gabata ba ciniki, amma wannan shekarar dai ta fi rashin ciniki. Duk da cewa kasuwa ta cika, amma shekarun baya ta fi haka cika; fiye da shekaru 30 muna wannan kasuwar Makola, idan ta cika babu masaka tsinke. Idan lokacin Kirsimeti ya kai, ana ciniki ne har ana rasa yadda za a amshi kudi (don yawan jama’a)."

A cikin wannan watar Disamba ne almajiran kananan sakandare suke canza makarantu zuwa manyan sakandare. Kuma a wannan lokaci ne iyaye ke kashe kudade don siyan kayayyakin da yara ke bukata, musamman wadanda za su je makarantun kwana.

Su ma dillalan dabbobi sun koka da rashin ciniki, wanda suka dangana da tsadar dabbobi sanadiyar faduwar darajar kudin Cedi.

Malam Dauda yace, kasuwar dabbobi dai ya zo kasa wannan shekarar idan an kwatanta da bara.

Abdullahi da akafi sani da Liman yace dabbobi sun yi tsada domin kudin Cedi na Ghana ya fadi.

"Abin da ya sa dabbobin suka yi tsada shi ne, muna canja kudin ne daga Cedi zuwa CFA. Da yake muna kawo dabbobin daga Burkina Faso da Nijar, kuma darajar CFA ta tashi. A wancan shekarar da cedi 1000 za ka samu raguna, amma yanzu sai kana da cedi 3000. Haka kuma zaka iya samun akuya cedi 800, 600 amma yanzu sai kana da fiye da cedi 1000."

Kamar yadda masana suka ce, wannan rashin ciniki da ‘yan kasuwa ke fuskanta na da alaka da yanayin da tattalin arzikin kasar yake. Lallai, alamu sun nuna cewa ‘yan kasuwan na cikin wani hali na matsi da damuwa. Ya kamata gwamnati da masu masu ruwa da tsaki, su yi duba ga lamarin.

Saurari rahoton Idris Abdallah a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Bikin Kirsimeti: ‘Yan Kasuwa Da Dillalan Dabbobi Sun Koka Da Rashin Ciniki A Accra