Shugaban Amurka Joe Biden ya karrama Fafaroma Francis da babbar lambar yabo ta Shugaban kasa ta ‘Yanci da shugabanci.
Wannan lambar yabo ce mafi girma ga farar hula da shugaban kasar ya bayar.
Bayanin lambar yabon ya bayyana cewa Paparoma “haske ne na bangaskiya, fata, da kauna da ke haskakawa a fadin duniya.”
An shirya Biden zai gabatar da lambar yabon da kan sa ga Fafaroma a jiya Assabar a birnin Rome, a wata ziyarar da za ta kasance balaguronsa a kasashen waje na karshe na shugabancinsa.
To amma Biden ya soke yin tafiyar domin sa ido kan gobarar daji a California.
Fadar shugaban kasa ta White House ta ce Biden ya baiwa Fafaroman lambar yabon ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, inda suka kuma tattauna kan kokarin samar da zaman lafiya da rage radadin matsin rayuwa a fadin duniya.