WASHINGTON DC - Shugaban ya kuma ce za a sake gina gadar ta Francis Scott Key nan take duk da cewa zai dauki tsawon lokaci.
Ya kara da cewa ce zai tabattar masu gudanar da aikin sake gina gadar sun sami duk kayayyaki da suke bukata daga gwamnatin tarayya saboda ganin sun sake gina gadar.
A safiyar yau, Talata ne wani jirgin ruwan mai dakon kwantena ya kutsa cikin wata babbar gada da ke Baltimore a jihar Maryland, lamarin da ya yi sanadin karyewarta.
Ku Duba Wannan Ma Gadar Baltimore Ta Dare Bayan Jirgin Ruwa Ya Ci karo Da ItaMotoci da dama sun fada cikin ruwan mai tsananin sanyi, kuma da farko masu aikin ceto sun fara neman akalla mutane bakwai ne.
An samu ciro mutane biyu daga cikin ruwan da ke karkashin gadar Francis Scott Key Bridge, inda daya na cikin mawuyacin hali, a cewar Shugaban hukumar yaki da gobara na Baltimore James Wallace.