Biden Da Zelenskyy Za Su Rattaba Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Tsaro A Taron Kungiyar G7

Biden - Zelenskyy

Shugaban Amurka Joe Biden da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ranar Alhamis, yayin da za su gana a Italiya a gefen taron kolin kungiyar kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya.

WASHINGTON, D. C. - Masu shawarwari daga kungiyar kasashen sun kuma cimma yarjejeniya kan yadda za a ba Ukraine kudi har dala biliyan 50 daga kadarorin Rasha da aka sanya wa takunkumi sakamakon mamayar da ta ke yi wa Ukraine.

Kungiyar kasashen masu karfin tattalin arziki na tattaunawa kan hanyoyin da za a yi amfani da kudi sama da dala biliyan 260 na Rasha da aka sanya wa takunkumi, wadanda akasarinsu na a wajen kasar, domin taimaka wa Ukraine kare kanta daga mamayar shugaban Rasha Vladimir Putin.

Wani jami'in fadar shugaban kasar Faransa ya tabbatar da yarjejeniyar a ranar Laraba, yana mai cewa za a ba Ukraine yawancin kudaden a matsayin bashi daga gwamnatin Amurka, daga ribar kudaden na Rasha da aka sanya wa takunkumi.

Zelenskky

Wasu mutane biyu da ke da masaniya kan lamarin sun tabbatar da shirin.

Ana dai ci gaba da yin tattaunawar karshe gabanin taron don kammala tsara ka'idojin yarjejeniyar a hukumance.

-AP