Biden Da Harris Sun Bayyana Taken Yakin Zabensu

Joe Biden da Kamala Harris

Yayin gabatar da abokiyar takarar sa dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Democrats ya caccaki shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence akan kasa shugabanci na gari a lokacin annobar COVID-19, inda ya ce shi da Harris za su gyara barnar da aka yi.

Joe Biden, ya bayyana kafa babban tarihi, a yayin da yake gabatar da Sanata Kamala Harris, wadda ya zaba a zaman mataimakiyarsa a gangamin yakin neman zabe a Delaware.

Biden da Harris da dukan su suke sanye da takunkumin rufe fuska sakamakon annobar coronavirus, sun yi jawabai a dandalin taron a makarantar sakandaren garin Biden na haihuwa wato Wilmington.

Jawaban nasu sun mai da hankali ne akan taken yakin neman zabensu, suna masu jaddada cewa shugabancinsu zai taimakawa Amurkawa a lokutan annoba da ci gaban komadar tattalin arziki. Sun kuma bayyana hikimar da ke tattare da zaben Harris.

A hukumance Biden ya bayyana Harris a matsayin ‘yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jiya Talata, lamarin da ya sa ta zama mace bakar fata ta farko da aka baiwa wannan tikitin a babbar jam’iyya.

Biden ya ce shi da Harris za su aiki wajen "sake gina kasa."

Ya caccaki shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence akan kasa shugabanci na gari a lokacin annobar COVID-19, inda ya ce shi da Harris za su gyara barnar da aka yi.