Benin Ta Sake Baiwa Nijar Izinin Soma Dakon Danyen Manta Daga Seme

Shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon

Ministan Ma’adinan jamhuriyar Benin a yayin wani ganawa da manema labarai yace kasarsa ta amince wa Nijar ta fara loda danyen man kan jirgin farko a matsayin matakin wucin gadi a bisa la’akari da yarjeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu.

Jamhuriyar Benin ta sake bai wa jamhuriyar Nijar izinin wucin gadi domin soma dakon danyen manta daga tashar jirgin ruwan Seme bayan da a makon jiya shugaba Patrice Talon ya hana tankoki daukan man da ya kamata Nijer ta fara shigar da shi a kasuwannin duniya.

Kasar China ce ta shiga tsakani a wannan dambarwa da ta samo asali daga matakin rufe iyakar da hukumomin mulkin sojan Nijer suka dauka a bisa zargin Benin da bai wa Faransa damar girke dakaru da nufin yi masu kutse zargin da Benin din ta ce ba shi da tushe.

Ministan Ma’adinan jamhuriyar Benin a yayin wani ganawa da manema labarai yace kasarsa ta amince wa Nijar ta fara loda danyen man kan jirgin farko a matsayin matakin wucin gadi a bisa la’akari da yarjeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu.

Seidou Adambe da ke samun danne gargada daga wani wakilin tawwagar kamfanin CNPC China ya kara da cewa kasar za ta yi iya bakin kokarinta don sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a yarjejeniyar da ke tsakanin bangarorin 3.

Ku Duba Wannan Ma Jamhuriyar Benin Ta Hana Jigilar Danyen Man Nijar Daga Tashoshinta

Da yake bayyana matsayinsa a kan wannan al’amari shugaban kungiyar SIEN ta ‘yan kasuwar Import Export Alhaji Yacouba Dan Maradi na cewa tun can farko Nijar ‘yar kallo ce a wannan rikici.

A karkashin jerin wasu yarjeniyoyin da suka hada Nijar da China da Benin ne Nijar ta shimifida bututun man da ya ratsa jihohin Diffa da Zinder da Maradi da Tahoua da Dosso yayinda ita ma a nata bangare Benin ta gudanar da makamancin wannan aiki daga iyaka zuwa tashar jirgin ruwan Seme da nufin soma fitar da danyen mai a tsakiyar watan nan na Mayu to sai dai juyin mulkin da aka fuskanta a Nijar ya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin gwamnatin Patrice Talon da hukumomin mulkin soja lamarin da ya shafi wannan haraka.

Ku Duba Wannan Ma Nijar Ta Maida Wa Jamhuriyar Benin Martani Kan Hana Jigilar Danyen Manta

Ganguna 90000 daga cikin 110000 da aka fara hakowa a kowace rana daga rijiyoyin Agadem na jihar Diffa ne Nijar ke aikawa tashar jirgin ruwan Seme akan hanyar cin kasuwannin duniya to sai dai hukumomin kasar Benin a wasikar da suka aike wa jakadan China a ranar 6 ga watan Mayun nan sun sanar cewa ba za su bari a fara lodin danyen man ba har sai mahukuntan Nijar sun bude iyaka da kasarsu.

A saurari cikakken rahoton Souleyman Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Benin Ta Sake Baiwa Nijar Izinin Soma Dakon Danyen Manta Daga Seme