Bazata Sake Zani ba Duk Daya ne Yanzu da Wancan Lokacin

Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya kenan Furfesa Attahiru Jega ke sanar da sakamakon zaben.

Kungiyar majalisar, Limaman masalatan Jumma’a, a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, ta mayar da martini akan shawarar da mi baiwa shugaban Najeriya...

Kungiyar majalisar, Limaman masalatan Jumma’a, a jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, ta mayar da martini akan shawarar da mi baiwa shugaban Najerfiya, shawara akan harkokin tsaro, kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya baiwa hukumar zaben Najeriya, data dage lokacin zaben kasar.

A wani taron manema labarai, da majalisar Limaman ta kira tace sam bata tare da wannan shawara, a ranar alhamis din nan ne dai aka ruwaito cewa Sambo Dasuki, yana bada wannan shawarar a wata cibiyar bincike birnin London, ta kasar Ingila.

Sakataren majalisar Limaman, Imam Umar Faruk, Yace “ Dage zabe ba zayyi maganin komai ba, a halin da ake ciki yanzu, bazata sake zani ba, duk lokacin da aka kai shi idan lokacin ya matso ‘yan takarar sunanan zasu sake fitowa wanda ke kai bai so ya sauka saboda haka da yanzu da wancan lokacin duk daya ne, yanzu ne ma muka san mai muke ciki gobe mai zai faru Allah kaidai ya sani, maganin alamarin nan ayi gaskiya.”

A halin da ake ciki dai majalisar Malaman, dace ta dukufa wajen gabatar da hudubobi a Masallatai na Jumma’a, dake jihar ta Neja domin nuna mahimmancin yin zabe lafiya.

Imam Umar Faruk ya kara da cewa “ Zamu je mu gana da Limamai ‘yan uwan mu dake sauran yankuna akan cewa su mayar da hankali wajen fadakar da jama’a, koda ranakun zabe yazo , mutumin da duk ya dogara ga Allah, in ma anyi wani abu da suke gani ba daidai ba daya shafi zalunci ko rashin gaskiya, toh azzalumi Allah ne ke da maganin shi.”