Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bayanin cewar Najeriya tana fama da talauci a sanadiyyar matsalolin tattalin arzikin da gwamnatin sa ta taras.
Wannan jawabi ko shakka babu ya jawo cece kuce inda jam'iyyar PDP ke ta nuna cewar bai kamata a yiwa kasar wannan fallasa ba domin zai iya firgita masu shi'awar zuba jari a Najeriya.
A kan haka ne wakilin sashin Hausa Umar Faruk Musa ya tattauna da wani kwararre akan harkokin tattalin arziki malam Shu'aibu Idris domin jin karin bayani akan ko nwadannan kalaman da shugaban kasa yayi zasu firgita masu shi'awar zuba hannun jari a kasar.
Malamin ya yi bayanin cewar "shugaba ko wani jigo a cikin gwamnati wanda yake rike da wani mukami, akwai maganganun da ya kamata ya yi, akwai kuma wadanda ko da ya san su bai kamata ya yi su ba. A duk lokacin da aka ce misali, ministan kudi, ko shugaban babban bankin Najeriya, ko kuma shugaban kasa ya fito ya ce kasa ta talauce ko bazata iya biyan albashi ba lallai abu ne mai matukar tsoratarwa duk da kuwa gaskiya ce suka fada".
A fannin jam'iyya mai mulki kuma, Malam Garba Shehu, kakakin shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wa wakilin sashin Hausa cewar wannan bayanin da shugaban Kasar ya yi gaskiya ne domin kuwa shi mutum ne da aka zabe shi kan gaskiya kuma ba lallai ne yazo ya fada ma duniya karya ba.
Daga karshe kakakin ya bayyana cewar dukkan masu zuwa zuba hannun jari wasu kasashe kan yi anfani da kwararrun masan harkokin tattalin arziki su bincika masu yanayin tattalin arzikin kasa kafin su zuba jari dan haka babu yadda za a yi masu karya, kuma ga shi jama'a na yi wa shugaba Buhari kirarin mai gaskiya! dan haka bai kamata ya yi karya ba.
Ga cikakken rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5