Bayanan Da Ake Yadawa a Kaina Kage Ne- Al Mustapha

Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.

Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.

Tsohon mia tsaron lafiyar marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al Mustapha, y ace duk bayanan da ake yadawa akansa game da cewa an kama shi a Afrika ta Kudu game da batun sayen makamai duk kage ne.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai, Al Mustapha ya ce ba a tsare shi a Ghana ba a wata makaranta da ake koyar da masu koyon harbi ba.

“An ce an kama ni a Afrika ta Kudu, ni nkuma ina nan a Najeriya, ina tsakanin Abuja da Kano da Yobe, an ce ina horar da mutane akan a hana zabe, wannan karya ce ta fitan hankali, shi Janar Buhari uba ne a wurinmu, kuma duk abin da za mu yi a matsayinmu na ‘ya’ya za mu yi,ba sai an ce ka yi ba.” Inji Al Mustapha.

Game da batun an kama shi a Ghana, Al Mustapha ya ce labarin kirkiro shi aka yi “kamar yadda wani malami a Kaduna ya yi ta yi kwanakin baya.”

Game da yadda ya gudanar da ayyukansa a lokacin gwamnatin Janar Abacha, Al Mustapha ya ce sun yin aikin su ne tsakani da Allah ba da ganin idon wani ba.

Ya kuma kara da cewa mutane da dama sun ci amanar marigayin, yana mai cewa akwai ynkurin juyin mulki da dama da aka yiwa Abacha amma ba kowanne ba ne ‘yan Najeriya suka sani.

“A kasar nan babu wanda ya taba yafewa idan aka yi juyin mulki sai Janar Abacha, yafewar da ya yin a farko shi ne a 1994, ya sallame su suka tafi ya gargadi wasu, daya daga cikin Janar din ma ya rubuta littafi ya kara tantance gaskiya cewa yunkurin juyin mulki suka yi, amma Abacha ya yafe musu” Inji Al Mustapha.

Ga karin bayani a wannan tattaunawar da suka yi da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Bayanan Da Ake Yadawa a Kai na Kage Ne- Al Mustapha- 4’19”