Bayanai Sun Nuna Trump Ya Nemi Jami'an Ukraine Su Binciki Biden

Wani takaitaccen bayanin tattaunawar da aka yi ta wayar tarho tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy, ya nuna Shugaba Trump ya bukaci a sa jami’an kasar Ukraine su yi bincike kan tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden.

‘Yan jam’iyyar Demokarat sun ce wannan takaitaccen bayanin da fadar White House ta fitar, ya tabbatar da zaton da dama ake yi cewa Shugaba Trump na gudanar da harkokin wajen Amurka ta yadda zai amfana a siyasance.

To sai dai Shugaba Trump ya yi shakulatin bangaro da duk wani zargi na cewa, akwai wani abin da ya furta a wannan tattaunawar da bai dace ba.

Haka zalika, wasu ‘yan jam’iyyar Republican da dama sun kare Shugaba Trump jiya Laraba, da cewa bayanin bai nuna an aikata wani laifi ba.

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala wata ganawa ta bai daya da Shugaba Zelenskiy a bayan fagen babban taron Majalisar Dinkin Duniya a Birnin New York da yammacin jiya Laraba, Trump ya ce ya na goyon bayan kokarin da Shugaban na Ukraine ya ke yi na magance dinbin almundahana, sannan ya sake zargin Biden da dansa Hunter da aikata rashin daidai.