Bayan Shekaru 240 Tana Gudanar da Mulkin Dimokradiya A Karon Farko Amurka Ta Samu Mace A Matsayin 'Yar Takarar Shugabar Kasa

Hillary Clinton macen farko da da wata babbar jam'iyya zata tsayar a matsayin 'yar takarar shugabancin kasar Amurka

Hillary Clinton ta shiga tarihi yayinda ta zama mace ta farko da wata babbar jam'iyya zata tsayar ta yi takarar shugabancin kasar Amurka

Jiya jam'iyyar Democrat ta tabbatar da Hillary Clinton a matsayin 'yar takararta bayan da Sanata Bernie Sanders yace a jingine dokokin taron a gabatar da ita.

Kasar Amurka dai tayi shekaru 240 tana bin tafarkin dimokradiya kuma ba'a taba tsayar da mace tsayawa takarar shugabancin kasar sai a wannan karon.

'Yan Democrats a wurin fidda 'yar takara a birnin Philadelphia

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Bayan Shekaru 240 Tana Gudanar da Mulkin Dimokradiya A Karon Farko Amurka Ta Samu Mace A Matsayin 'Yar Takarar Shugabar Kasa - 10' 14"