Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Jam'iyyar Demokrat A Nan Amurka Ta Fara Taron Fidda Dan Takara


Taron jam'iyyar Demokrat a Philadelphia
Taron jam'iyyar Demokrat a Philadelphia

Kamar yan jam'iyyar Republican da suka yi taron fidda dan takara makon jiya ita ma jam'iyyar Democrat ta fara nata taron yau a birnin Philadelphia inda zata fidda nata dan takara ko 'yar takara domin karawa da Donald Trump a zaben shugaban kasa da za'a yi watan Nuwamba mai zuwa

Yu ake fara babban taron jam'iyyar Demokrat anan Amurka a birnin Philadelpha dake jihar Pennsylvania da suka sama taken: Hadin kai.

Jami'iyyar na son jaddada bukatar hadin kai a wannan zamanin.

Muhimman mutane ne zasu gabatar da jawabai a yau din da suka hada da matar shugaban kasar Amurka Michelle Obama da Bernie Sanders wanda ya fafata da Hillary Clinton a zaben fidda gwani da wata Artis Sylver wadda ta zo kasar Amurka tana 'yar shekaru hudu tare da iyayenta.

Ita Sylver har ta gama karatun sakandare bata da takardar izinin zama Amurka saboda haka duk wani yunkuri da tayi na shiga yin wani abu sai iyayen su ce mata a'a. Bata san dalilin da ya sa suna hanata ba sai da ta gane cewa basa son ta shiga ne domin kada mahukunta su gane cewa sun shigo kasar ta barauniyar hanya ce.

Magoya bayan Bernie Sanders
Magoya bayan Bernie Sanders

Yayin da Sanata Reid, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Amurka, yake kamfein sai ta cusa masa wasika inda ta bayyana masa halin da take ciki dalili ke nan da 'yan jam'iyyar demokrat suka dauki tarihinta suna yayatawa da zummar ganin an canza dokokin kasar kan irin mutane kamarta. 'Yan jam'iyyar na son nuna banbanci tsakaninsu da Trump na jam'iyyar Republican wanda yake son a gina katangar shinge kasar daga Mexico.

Su 'yan demokrat suna son duk wanda ya shigo kasar a bashi daman nuna irin tashi baiwar da hazakar da yake da ita domin gina kasa ba a koreshi ba.

Zauren taron a Philadelphia
Zauren taron a Philadelphia

A karon farko ba shugabar jam'iyyar zata jagoranci taron ba bayan ta buga kararrawar bude wa. Da zara kuma an kammala taron zata yi murabus saboda wasu wasikun email da wata kafar kwarmato ta internet ta buga wadanda suka ce wasu cikin shugabannin jam'iyyar suna goyon bayan Hillary Clinton maimakon su zama 'yan ba ruwanmu. Cikin wasikun har an zargi Bernie Sanders da kasancewa Bayahuden da bashi da addini. Fallasar tamkar tabbatar da abubuwan da shi Bernie Sanders ya sha fada ne lokacin da suke fafatawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG