A yau rana ta biyu, banda jawabai da aka saba gabatarwa, za'a fara kirga kuri'un tabbatar da ita Hillary Clinton a matsayin 'yar takara da zata kasance mace ta farko da ta tsaya zaben shugabancin Amurka.
Cikin wakilan, Bernie Sanders, wanda ya ja sosai da Hillary Clinton, yana da wakilai 1850 kuma ba'a sani ba ko zasu amince da Hillary Clinton, wato ko zasu rungumi kadara.
Taken taron na yau shi ne yaki domin kananan yara da iyalai har tsawon rayuwarsu inda tsohon shugaban kasar, kuma maigidan Hillary Clinton, wato, Bill Clinton, zai bayyana yadda matarsa ta tashi a tsawon rayuwarta tana tallafawa yara da iyalai domin ganin ta inganta rayuwarsu.
Mata da suka kafa wata kungiyar kula da yara da iyalai da mutunta rayuwan 'ya'yansu da dangin wadanda aka harbe zasu gabatar da jawabai. Zasu nuna yadda rayuwarsu ta canza da kuma yadda Hillary Clinton ta taimaka masu.
Bisa ga alamu jam'iyyar ta kama hanyar dinke barakar da ta kunno kai saboda magoya bayan Sanders da ake kyautata zaton zasu tada kayar baya basu yi ba.
Ga karin bayani.