A zantawar da yayi da Muryar Amurka gwaman jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana irin ayyukan sake gina wasu garuruwa da suka yi, kuma zasu cigaba da yi har duk mutanen dake gudun hijira sun samu sun koma matsuguninsu.
Yace kama daga hanyar da ta nufi Damaturun jihar Yobe sun gina gidage fiye da dari biyu a garin Maitakolori da Kamsukau inda suka ginawa mutanen garin gidajensu da asibitocinsu da masallatansu. Haka ma suka yi a Auno da Mayinok da Mgamdu.
A can garin Benishaikh sun gyara sakatariyarsu da barikoki. Duk abun da ya cancanta a yi, an yi a garuruwan saboda mutane su samu su koma cikinsu da zama.
Gwamna Shettima yace ko ta halin kaka zasu yi kokari su gina garuruwan. Baicin haka wanshekaren sallah zai kwashe nashi-inashi ya tare a Bama tare da gwamnatinsa kuma sai ya ga abun da zai tubewa Buzu nadi. Yace zasu ga yadda za suyi su gina Bama.
Gwamnan yace zai sa ido akan sake gina Bama saboda a ba mutane matsugunin da zasu koma. Yace muddin Shugaba Buhari na kan mulki yayi imanin zai taimaka masu.
Ga firar da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5