Bauchi: An Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali a Wasu Mazabu

Zabe a Jihar Bauchi

A jihar Bauchi sake zabukan da ba a akammala su ba a yankunan kananan hukumomin jihar ya gudana cikin yanayi mai kyau musamman ma idan akayi la’akari da samun yawan fitowar mutane masu son kada kuri’a.

Sai dai kuma rahotanni na nuni da cewar an samu matsalar sace akwatunan zabe a wassu mazabun da hakan ka iya kawo cikas ga batun samun sahihin sakamakon kuri’u a wadannan wurare.

Kamar yadda ake hasashe dangane da sake zaben da hukumar INEC ta yi, jama’a sun fito maza da mata domin kada kuri’unsu.

Wani dan kungiya mai zaman kanta dake aikin sa ido ga shirin zaben a karamar hukumar Bogoro, ya bayyanawa Muryar Amurka ta wayar talho yadda yaga zaben ya gudana, inda ya ce ya zuwa lokacin da yake magana ana gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

A daya gefen kuma, a shiyyar Katagum musamman garin Azare jama’a sun bayyana kuma zabe na gudana, saidai ana cikin gudanar da zaben sai jami’an tsaro tare da shugaban riko na karamar hukumar suka bayyana a mazabar Cara-cara anan sai labari ya canza, kamar yadda wassu ganau suka bayyana.

Sai dai duk kokarin da Muryar Amurka ta yi domin jin tabakin bangarorin yan sanda da kuma shugaban karamar hukumar katagum din ya ci tura.

Your browser doesn’t support HTML5

Bauchi: An Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali a Wasu Mazabu - 3'26"