Gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya musanta zargin da wasu ke yi na cewa kuntatawar da yake yiwa mataimakinsa, Alhaji Nuhu Gidado ne ya sa mataimakin nasa ya yi murabus.
A ranar Larabar da ta gabata Gidado ya yi murabusa daga mukaminsa inda ya mika takardar ajiye aikinsa ga Sakataren gwamnatin jihar.
Jaridar Daily Trust a shafinta na yanar gizo ta ruwaito kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, yana cewa, kakakin tsohon mataimakin gwamnan yana cewa dalilin da ya sa ya yi murabus shi ne saboda ba a kyautatawa Gidadon.
Amma gwamna Abubakar ya musanta wannan zargin, yana mai cewa, “sau biyu idan zan yi tafiya, ina mikawa majalisar jiha wasikar mika mulki ga mataimakin nawa domin ya rike jihar a matsayin mukaddashin gwamna.”
“Baya ga haka, na ba shi rikon ma’aikata mafi muhimmanci, wato ma’aikatar ilimi, inda nake zuba mafi aksarin kasafin kudinmu tun daga 2008.” Ya kara da cewa.
Ita ma jaridar Guardian, wacce ta ruwaito labarin na NAN, ta wallafa a shafinta na yanar gizo inda ta ce, gwamna Abubakar ya kara da cewa, “ya kamata mutane su tsaya su karanta daukacin wasikar da ya mika, za a ga cewa bai ambaci wani abu mara dadi da ya faru ta sakninmu ba.”
Murabus din Alhaji Gidado ya janyo cece-ce-ku-ce a jihar ta Bauchi wacce ke arewa maso gabashin Najeriya da ma sauran sassan kasar, saboda, ba kasafai ake samun masu rike da madafun ikon suna yin murabus daga mukamansu a kasar ba.