Yanzu haka mutanen Najeriya da sauran yankunan Afrika na ta fadin albarkacin bakinsu kan inda ya kamata sabuwar gwamnatin Najeriya ta sa gaba
A farkon makon nan hukumar zabe ta bayyana Janar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon da ya gabata inda ya ka da shugaba mai ci Dr. Goodluck Jonathan.
“Na farko shi ne zaman lafiya ya dawo a cikin Najeriya, wato wannna matsala da ke gare mu ta Boko Haram, ya shawo kanta, na biyu matsalar zaman kashe wando na uku a dinga adalci a cikin iko.” In ji Farfesa Boube Namaiwa na jami’ar Cheikh Anta-Diop da ke Dakar a Senegal.
Farfesan ya kara da cewa, akwai bukatar Buhari ya tunkari batun cin hanci da rashawa a kasar sannan ya tuna cewa ta hanyar kuri’u ya samu mulki ba ta hanyar juyin mulki ba duk da cewa yaki da rashawa na bukatar irin jajircewar da ya nuna a farko.
“Muddin dukka wadannan suka samu, to Najeriya za ta zama daya daga cikin kasashen duniya masu fada a ji.” In ji Farfesa Namaiwa.
Your browser doesn’t support HTML5