WASHINGTON, DC —
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, wato (NFF) ta bayyana cewa ‘yan kungiyar “Golden Eaglets” a yau zasu tashi zuwa kasar Argentina.
Hukumar tace batun takardun tafiya ne da suka hada da Visa, ya kawo jinkiri, ‘yan kungiyar dai zasu kasance a Argentina, a wani mataki na shirye shiryen na cin kofin kwallon kafa na duniya na ‘yan kasa da shekari 17, wanda za’a yi a kasar Chile a wannan watan.
Sakatare janar na hukumar ta (NFF) Muhammad Sanusi, yace ‘yan kungiyar sun kunsi mutane 25, ne.
Yan Golden Eaglets, suke rike da kofi a halin yanzu, zasu kuma hadu da kasashen Croatia, Amurka da kuma mai masaukin baki Chile.