Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Mako Daya Shafin Facebook Ya Samu Tangarda Sau Biyu


facebook
facebook

A jiya litinin da yamma, a karo na biyu cikin sati daya shafin zumunta na facebook, yasamu wata ‘yar-tangarda, wadda ta sa mutane da dama basu iya shiga shafin zumuntar, na tsawon wasu awowi. Wannan yasa hannun jarin kamfanin ya sauka da kashi hudu 4%, akan kudi dallar Amurka $89.25 dai-dai da naira dubu goma sha takwas 18,000, a kasuwar cinikayya.

A rahoton da wani shafi Downdetector.com, ya fitar dake lura da irin katsalandan din da shafin kamfanin ya fuskanta, ya nuna cewar anfi samun wannan matsalar ne a yankin arewacin kasar Amurka. A wannan tsakanin, shafin na wayar hannu shima ya dena aiki wanda bangaren sakon gaggawa ne kawai yayi aiki a lokacin.

Mutane da dama idan sukayi kokarin shiga shafin, sai ace musu kuyi hakuri wani abu na tafiya ba dai-dai ba a shafin. Hakama a ranar Alhamis da ta gabata, hakan ya faru wanda ya shafi kasashe yankin Turai, India, da Australia.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG