Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarauniyar Ingila Ta Rubuta Wasika Ga 'Yar-Shekaru Shida


Sarauniyar Ingila Elizabeth
Sarauniyar Ingila Elizabeth

Sau nawa kukan rubuta ma shugabannin ku wasika, kuma su rubuto muku amsa? Ko da kuwa shugabannin siyasa, addini, sarauta, da dai makamantan hakan. A karon farko wata yarinya mai suna Melissa, ‘yar shekaru shida 6, da haihuwa, ta rubuta ma sarauniyar Ingila wasika.

Tace da farko ina so nayi amfani da wannan damar, don tayaki murnar zama sarauniya da tafi kowace dadewa a kan gadon mulki. Kuma ina so nayi amfani da wannan damar, don na gayyace ki bukin zaga yowar ranar haihuwa ta “Birthday” a turan ce, na cika shekaru bakwai 7. Melissa, ta kokarta wajen zana hoton sarauniya a jikin katin gayyata da ta aika ma sarauniya.

Abun sha’awa a da labarin shine, yadda sarauniyar Ingila Elizabeth, ta umurci wata ta hannun damar ta, da ta rubuta ma Melissa, amsar wasikar ta. Ta rubuta cewar, Melissa, sarauniya ta umurce ni da na rubuta miki, wannan wasikar a madadin ta. Kuma ta umurce ni da na baki hakuri, domin bazata samu damar zuwa wajen bukin haihuwar ki ba, domi kuwa tana da wasu abubuwa masu yawa a gaban ta, amma tayi alkawalin zuwa kakar shekara mai zuwa, zata gayyace ki da iyayenki, don zuwa fadar sarauniya, don ganin irin kayan alatu da ke ciki. Ta kuma umurce ni da na aiko miki da wannan karamin littafin, da zai nuna miki kadan daga cikin tsarin gidan sarautar Ingila.

Ku rubuto muna ra’ayoyin ku danga ne da yadda kuke gudanar da mu’amala tsakanin ku, da shugabannin ku na kowa ne mataki a shafin mu na dandalinVOA.com

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG