Manoman tattasai a jihar Diffa dake jamhuriyar Nijar, sun kira ga gwamnati da ta taimaka musu su koma noman su da ya samu tsako sanadiyar matsalar boko haram, ganin an dan samu sauki na tashin hankalin da jihar tayi fama da shi a baya.
Noman tattasai na cikin abinda jihar Diffa, ta shahara dashi inda kasuwanci shi ya tsallaka zuwa kasashe makwantan Nijar, sai dai a yanzu haka harkar tattasai ya ja baya sanadiyar matsalar kungiyar ‘yan Boko Haram, da jihar ta Diffa tayi fama da ita in ji Musa Gwani Bagara wakilin masu noman tattasai a Diffa.
Ya kara da cewa tattasai yanzu ba kamar yadda yake da ba yake saboda babu shi sosai dalili kuma shine batun masu tada kayar baya da suka addabi jama’a, abinda ya kuma sa farashin ya fada da fiye da kashi hamsin na yadda ake saida shi da, wanda bai rasa nasaba da rashin zuwan masu siyan kayan.
Amma ganin cewa rigingimun sun yi sauki yanzu haka manoman tattasai a bagarorin biyu watau Najeriya da Nijar sun fara sharan gona domin fara noma.
Ya kara da cewa koda yake Gwamnati tayi alkawarin taimakawa amma kawo yanzu babu amo babu labari zai dai zaman jiran tsammani.
Your browser doesn’t support HTML5