Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gayyaci Jakadan Turkiyya Kan Tashin Hankalin Da Ya Faru


Dogarawan shugaban Turkiyya na dukan masu zanga-zanga a Amurka.
Dogarawan shugaban Turkiyya na dukan masu zanga-zanga a Amurka.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gayyaci jakaden kasar Turkiya bayanda dogarawa, da magoya bayan shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan suka lakadawa masu zanga zanga duka a kofar ofishin jakadancin Turkiya farkon wannan makon.

Wani jami’in ofishin ma’aikatar harkokin wajen Amurka yace jakaden Sedar Kilic ya gana da mataimakin sakataren ma’aikatar Thomas Shannon jiya Laraba, kwana daya bayan tashin hankalin da aka yi a ofishin jakadancin.

Kakakin ma’akatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace, “tashin hankali ba shine hanyar da ta dace ta maida martani ga fadin albarkacin baki ba, muna goyon bayan ‘yancin al’umma a ko’ina, na bayyana ra’ayoyi da kuma gudanarda zanga zangar lumana. Ta kara da cewa, “Muna sanar da gwamnatin kasar Turkiya damuwarmu da kakkausan lafazi.

Saneta John MacCain na jam’iyar Republican, shugaban kwamitin ayyukan soji na majalisa, yace yana son ganin an dauki mataki mai tsauri.

Ya shaidawa wani shirin tashar talabijin ta MSNBC da aka yayata jiya alhamis cewa, “Ya kamata mu kori jakadensu daga Amurka”.

Ofishin jakadancin ya dora alhakin tashin hankalin kan kungiyoyi dake da alaka da jam’iyar PKK, ta kasar Turkiya da cewa, sun tunzura Amurkawa ‘yan asalin kasar Turkiya da suka taru domin yiwa Erdogan gaisuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG