Wadannan dokokin dai sun hada da 'yancin mata, da battuttuwan da suka shafi matasa, du kuma masu bukata na musamman, batun cin gashin kai na kananan hukumomi, da kafa 'yan sandan jihohi da dai wasu al'amura da ake ganin cewa lalle sai an sake lale.
Sai dai tuni dai wasu 'yan jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Najeriya suka nuna sha'awarsu na gabatar da wannan zauren da suke neman canji a kai.
A hirar shi da Muryar Amurka, Ambasada Ahmed Shehu shugaba kungiyoyin masu zaman kansu na jihar Borno, ya ce tun shekara goma sha daya ne ake ta abu daya. Ya kamata a zauna a sake tunani menene ba'a yi dai-dai ba. Ya kara da cewa daya daga cikin dalilan shine sarakuna ba sa cikin kundin tsarin kasar, wannan shine ya sa a ke cutar jama'a domin basu da murya.
Karin bayani akan: jihar Borno, Muryar Amurka, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A nata bayanin Hassana Maina, wata 'yar gwagwarmaya ta bayyan cewa ta na so ta ga yadda za a daina cin zarafin mata musamman fyade da ake musu. Bisa ga cewar ta, wanan dama ce da za a kare hakkokin mata a kuma hukumta masu laifi.
Mutanen da Muryar Amurka ta yi hira da su suna gani za a iya amfani da wannan damar wajen gyara matsalar tsaro, sannan kuma a rage karfin da gwamnoni ke da shi don sukan yi amfani da shi su maida talakawa bayi.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5