Yayin da ya rage 'yan kwanaki a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na jihohi a Najeriya, wasu ‘yan jam’iyyar APC, magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Adamawa, sun ce wannan karo babu batun SAK a zabe, za su duba cancanta.
Hakan ya biyo bayan lashe zaben Shugaban kasa da jam’iyyar adawa ta PDP ta yi a jihar, batun da ya sa kusoshin jam’iyyar APC a jihar musayar kalamai.
A zaben shekarar 2015 guguwar SAK ta taka gagarumar rawa wajan zabe, amma da alamu a wannan zaben da ke tafe ranar Asabar 9 ga watan Maris, za ta sauya zani musamman a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Adamawa.
Kungiyar Northeast Buhari Support Group ta kira taron manema labarai a birnin Yola, inda ta taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben shugaban kasa karo na biyu, da kuma bayyana aniyar kungiyar na dole abi cancanta a wannan karon ba jam’iyya ba, a cewar darakta janar na kungiyar Aliyu Usman Waziri.
To a martanin da jam’iyyar APC ta mayar ta hannun sakataran tsare tsaren jam’iyyar a jihar Adamawa, Ahmad Lawal, ta ce "duk wanda yace zai yi shinkafa da wake to ba dan jam’iyyar APC ba ne saboda duk wani dan APC ya kamata ya bi dokar shugaban kasa Muhammadu Buhari da y ace ayi APC SAK daka sama har kasa.”
Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar adawa ta SDP a jihar Adamawa, Chief Emmanuel Bello ya ce shi bai janye wa ko wane dan takara ba kuma jam’iyyar ba ta shiga hadaka da wani dan takara ba.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-Aziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5