Zaben kananan hukumomi a Najeriya kan zo a lokuta daban daban a juhohin kasar, inda akan samu gwamnoni ke nada kantomomi gabanin a yi zabe.
WASHINGTON D.C. —
Wani abin lura anan shi ne duk kananan hukumomin jam’iyyar da gwamna ke ciki ne ke lashe zaben har ma da na kansiloli.
Hakan na faruwa ne koda mutane na kukan cewa gwamnoni ba su yi adalci ba, wandanda suma ake musu kallon magudi ne kawai ke ba su damar lashe zabe.
Shugaban Najeriya ya nuna takaicinsa bisa irin wannan tsari wanda za a ce jam’iya guda ta lashe dukkanin kujerun kananan hukumomi.
Magudin zabe a Najeriya ba sabon abu bane, sai dai a baya baya nan amfani da na’urar tantance katin masu kada kuri’a ya sauya lamarin.
Saurari wannan rahoto na Nasiru Adamu El Hikaya domin jin karin bayani game da wannan batu:
Your browser doesn’t support HTML5