Gangamin da matan su kayi a kauyen Kwali dake yankin babban birnin Tarayya Abuja, can kusa da iyakar jihar Kogi, ya mai da hankali kan karawa ungozoma ilimin kula da matan da akayiwa kaciya in sun zo haihuwa.
Masana daga hukumar kula lafiya matakin farko ta Abuja, sun bukaci jami’an Ungozoman suke garzayawa da irin matan Asibiti, maimakon karbar haihuwar a gida. Kaciyar dai inji masana akan yi tane da zummar hana matan fasikanci kafin su yi aure, wadda hakan kan juye ya zama babbar illa.
Samun karin irin wannan mata da akayiwa kaciya a Asibitoci ya sanya zama wajibi a rika shirya irin wannan taro na musammam a karkara. Kunya na irin matan da suka samu irin wannan illa, kasa ba a ganosu cikin lokaci sai lamarin ya ta’azzara.