Batun Karkatar Da Tashi Da Saukar Jiragen Saman Abuja Zuwa Kaduna

Babbar Tashar Jirgin Saman Birnin Abuja

Masana da masu ruwa da tsaki kan harkokin sufurin jiragen sama da tsaro sun fara mayar da martani game da matakin gwamnatin Najeriya na rufe filin jirgin saman Abuja, da kuma bada damar ‘daukar makamai ga jami’an tsaron filin jirgin sama a kasar.

A wata sanarwa da Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya bayar a Abuja, yace a ranar 8 ga watan Maris ne za a rufe babban filin jirgin saman Abuja, tare kuma da maida zirga-zirgar jiragen zuwa babban filin jirgin sama na jihar Kaduna.

Ministan yace wannan mataki ya zama wajibi domin gudanar da gararraki a filin jirgin saman na kasa da kasa a Abuja, wanda shekaru 15 da suka gabata yakamata ace anyi gyaran amma hakan bai samu ba. yace daukar wannan mataki ya zama dole domin ceto rayukan al’umma dake cikin hatsari a yayin tashi da saukar jiragen sama.

Bisa ga la’akari ga yawan zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Abuja, Ministan yace gwamnatin Najeriya ta ware kudi Naira Biliyan 1.1 domin gudanar da gyara a filin jiragen sama na Kaduna.

Manajan daraktan gudanarwa na kamfanin Azman Air, Alhaji Sulaiman Lawal, yace tunda matakin gyara ne wannan ci gaba ne na kasa baki ‘daya, amma barin filin saukar jirage babu gyara hatsari ne ga rayuwar mutane.

Daukar matakin karkatar da tashi da saukar jirage daga Abuja zuwa Kaduna ya janyo sharshi daga masana harkokin sufurin jiragen sama, wadanda ke ganin kamata yayi ayi amfani da filin jirgin saman Minna, wanda ya fi kusa da birnin Abuja.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

Your browser doesn’t support HTML5

Batun Karkatar Da Tashi Da Saukar Jiragen Saman Abuja Zuwa Kaduna