Batutuwan ilimi da ilimin ‘yan mata da almajirai da matsalar shaye-shaye da matasa ke yi, na daga cikin manyan matsalolin da suka mamaye lardin Arewacin Najeriya. game haka ne kungiyoyin rajin ci gaban mata da yara kanana, da kuma cibiyoyin nazari da bincike kan harkokin rayuwar iyali ke shan alwashin ribanya kokarinsu wajen cimma muradunsu a wannan shekara ta 2017.
Daraktar cibiyar nazarin jinsin bil Adama da inganta rayuwar iyali ta jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Aisha Abdul Isma’il, tace a bana cibiyar na da tsare-tsaren cimma muhimman muradun da ta saka a gaba. Ta kara da cewa la’akari da yawa da kuma nauyin aiyukan da suka rataya a wuyan cibiyar, ya sanya take kokarin kulla kawance da sauran hukumomi da cibiyoyi don cimma nasara.
A shekarar da ta gabata ne aka gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki kan kalubalen cin zarafin kananan yara da mata, wadda cibiyar bincike kan lamuran dimokaradiyya ta Mambayya a jihar Kano ta shirya.
Malama Hauwa Ibrahim El-Yakubu, guda cikin wakilan da suka halarci taron tace a wannan shekara ta 2017 hukumomi da kungiyoyi ya kamata su himmatu wajen aiwatar da abubuwan da taron ya cimma.
Domin karin bayani ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.