Tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce biyan ‘yan bindiga kudaden fansa a duk lokacin da suka yi garkuwa da mutane, ba ita ce maslaha ga kasar ba.
Kafofin yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito Obasanjo yana cewa, akwai bukatar gwamnati, ta kirkiri wata hanya ta magance matsalolin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, maimakon ba su kudin fansa.
“Gwamnati ta sha biyan kudin fansa. “Gwamnati ta sha biyan kudin fansa. Ba wannan gwamnati mai ci kadai ba, har a zamanin mulkin Jonathan ma sun biya kudin fansa, amma suna musantawa.”jaridar Punch ta ruwaito Obasanjo yana cewa.
Obansanjo wanda ya mulki Najeriya karkashin tsarin dimokradiyya daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya kwatanta yin hakan a matsayin “wawanci.”
Tsohon shugaban na Najeriya ya yi wadannan kalaman ne yayin da wasu mambobin kungitar kwararru ta ‘yan kabilar Tibi daga jihar Benue, suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun a ranar Laraba.
Obansajo ya ce shi bai amince a rika biyan ‘yan bindiga kudin fansa ba, domin yin hakan, yana kara masu kwarin gwiwa ne kawai.
Ya kara da cewa, ya zama dole gwamnati ta dauki wasu tsauraran matakai wajen tunkarar ‘yan bindigar.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El Rufai, ya sha nanata cewa bai amince da yin sulhu da ‘yan bindiga da kuma biyan kudin fansa ba, matakin da ya janyo mai suka da yabo.
Daliban kwalejin gandun daji da ke Afaka 27 da aka sako a ranar Laraba a jihar ta Kaduna, sun kwashe sama da kwana 50 a hannun ‘yan bindiga kafin a sako su.
Har yanzu akwai daliban jami’ar Greenfield da ke hannun ‘yan bindigar wadanda aka sace su a ranar 11 ga watan Maris duk a jihar ta Kaduna.
Baya ga haka, akwai daidaikun mutane da ake garkuwa da su a sassan na Najeriya, wadanda iyalansu ke biyan kudin fansa a sako su.
Dangane da masu kiran a raba Najeriyar, Obasanjo ya ce yin hakan ba ita ce mafita ba, yana mai nuni da cewa a rika tunawa da makomar kananan kabilu da ke kasar.
Gwamnati ta sha musanta cewa tana biyan kudaden fansa a duk lokacin da aka sako wadanda aka yi garkuwa da su, kuma ya zuwa yanzu ba ta ce uffan ba, dangane da kalaman na Obasanjo.
Batun biyan kudin fansa ya janyo zazzafar muhawara a Najeriya inda yayin da wasu suke goyon bayan matakin, wasu kuwa gani suke ba farar dabara ba ce.
Ana zargin wasu gwamnatoci a jihohin arewa maso yammacin Najeriyar da biyan kudaden fansa ga ‘yan bindiga tare da yin sulhu da su, amma duk da haka suna fuskantar matsalar hare-hare daga ‘yan bindigar.