Batagari Sun Afkawa Fadar Sarkin Nupawan Lokoja A Jihar Kogi

Gwamna jihar Kogi Usman Ododo (Facebook/Usman Ododo)

An soke gudanar da bikin sakamakon mummunan harin bayan da al’ummar Nupawa daga makwabtan jihohi saku fara isowa a jajibirin kalankuwar.

Wasu batagari sun kaiwa fadar Sarkin Nupawan Lokoja, Emmanuel Dauda-Shelika, Nyamkpa na 4, hari tare da bankawa wata karamar motarsa da wasu kayayyaki masu daraja wuta a cikin gidansa.

Ana zargin cewar batagarin sun farwa fadar dake yankin New Layout na birnin Lokoja fadar gwamnatin jihar Kogi ne a daren asabar din data gabata da misalin karfe 1, inda basaraken ya sha da kyar ta hanyar tsallake katanga.

Harin na zuwa ne sakamakon shirin da al’ummar Nupawa mazauna Lokoja karkashin kungiyar bunkasa birnin na karbar bakuncin bikin kalankuwar Nupawa ta karshen shekara a karo na 2, mai taken: “Kalankuwar Al’adar Nupawan Lokoja ta 2024” da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Disamban da muke ciki.

An soke gudanar da bikin sakamakon mummunan harin bayan da al’ummar Nupawa daga makwabtan jihohi saku fara isowa a jajibirin kalankuwar.